Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu ranar daina lalacewar wutar lantarki musamman babban layin da ke kai wuta yankin arewa.

Ministan makamashi Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka yayin kare kasafin kudi na shekarar 2025 a gaban kwamitin majalisar dokoki kan makamashi.
Adebayo ya ce sakamakon rashin tsaro ya sa gwamnatin tarayya ba za ta iya tabbatar da ranar daina lalacewar wutar yankin arewa da kuma gyarawa ba.

A cewarsa, babban layin Kaduna zuwa Shiroro zu a Mando shi ne layi na biyu mafi girma da ke kai wutar lantarki arewa, kuma har yanzu ba a gyara ba saboda rashin tsaro.

A sakamakon rashin gyaran ne ya sa sauran layikan ke ci gaba da faduwa.
Ya ce a yanzu za a ci gaba da fuskantar yawan faduwar layukan wutar.
Ministan ya ce hadin gwiwar da su ka yi da ofishin mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu bai kawo karshen kalubalen da bangaren ke fuskanta ba.
Ministan ya ce su na shirin saka kyamarorin tsaro da fitilu masu amfani da hasken rana a wuraren da hanyoyin layin lantarki ya ketara domin magance matsalar a gaba.