Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce akwai yiwuwar ƙara kudin kiran waya da data da aika sakonni da kaso 30 zuwa 60.

Ministan sadarwa na ƙasa Dakta Bosun Tijani ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Channels.

Ministan ya ce sun karbi rahoto daga masu masana masu zaman kansu kan yadda karin zai kasance

Tun tuni ministan ya yi watsi da bukatar kara kudin da kaso 100 wanda kamfanonin sadarwa su ka bukata.

A cewarsa, za a yi karin kuma ba da jimawa ba amma ba zai kai da kaso 100 ba.

A makon da ya gabata aka fara wani zama da masu ruwa da tsaki kan batun, kuma aka bayar da umarnin nazartar buƙatar haka.

Kamfanonin sadarwa a Najeriya ne dai su ka ce ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukansu ba na tare da sun yi ƙari a kan kudaden kira da data da kuma na aika sakonni ba.

A cewarsu matukar ana buƙatar ingantaccen sadarwa a ƙasa to ya zama wajibi a yi karin kuɗaɗen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: