Wata gobara ta kone shanu da dabbobi da tsintsaye sama da 70 a Kano.

 

Gobarar ta faru ne a ƙauyen Danzago da ke karamar hukumar Danbatta a jihar

 

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis.

 

Ya ce gobarar ta faru jiya Laraba a gidan Ado Yubai.

 

Gobarar ta halaka shanu biyu, tinkiya 36 da awaki 19 sai kaji 10 da rumbu guda 19.

 

Bayan zuwansu sun samu nasarar ceto shanu guda biyu, tinkiyoyi guda huɗu sai kuma rumbu guda biyu da sauran kayan amfani.

 

Haka kuma gobarar ta shafi gidan wani Alhaji Ibrahim Mai Gariyo kuma a nan ma ta kone dakuna da dama da rumbu daya sai tinkiya takwas, akuyoyi uku.

 

Jami’an sun tseratar da rumbu guda daya yayin da jami’in hukumar ɗaya ya samu raunin ƙuna.

 

Zuwa yanzu jami’an na ci gaba da bincike don gano dalilin tashin gobara

Leave a Reply

%d bloggers like this: