Wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun hallaka mutum guda tare da jikkata wasu Shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungun ta Jihar Kebbi.

Lakurawan sun yi aika-aikar ne da misalin Karfe 11:00 daren Jiya Alhamis.

Shugaban Karamar Hukumar Argungun Aliyu Sani Gulma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wadanda maharan suka hallaka na kwance a Asibitin Tarayya da Ke Jihar.

Gulma ya bayyana cewa Lakurawan sun shiga yankin ne a lokacin da mafiya yawa daga cikin mutanen yankin sun shiga gidajensu domin yin bacci.

Shugaban karamar hukumar ya ce sun sanar da hukumomin tsaro faruwar lamarin, inda jami’an tsaron sojoji suka isa yankin don tabbatar da tsaro da lafiyar mazauna yankin.

Shima kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Nafi’u Abubakar ya tabbatar da faruwar harin.

Ya ce rundunarsu ta aike da jami’an ‘yan sanda na musamman gurin don tabbatar da tsaron yankin.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: