Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta sanya dokar takaita zirga-zirga daga karfe 12:00 na dare zuwa karfe 5:00 na safiyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Buhari Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.
Kakakin ya ce dokar za ta fara aiki ne daga yau Juma’a.

Acewarsa rundunar ta sanya dokar ne sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu akan barazanar tsaro a Jihar.

Buhari ya bayyana cewa batagarin na shirin aikata ta’addancin ne a cikin dare, wanda hakan ya sanya rundunar daukar matakin takaita zirga-zirgar.
Kakakin ya kuma bukaci da al’ummar Jihar da su guji karya dokar da aka sanya, don tabbatar da tsaron Jihar.
