Tsohon shugaban Najeriya a mulkin Soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa yayi dana sanin rushe zaben shugaban Kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Babangida ya bayyana hakan ne a a yau Alhamis a gurin kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’ a Abuja.

Acewar Babangida da zai samu wata damar da ya tabbatar da zaben.

Janar Babangida ya dauki laifin soke Zaben wanda ‘ƴan takara biyu tsaakanin Mashood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party SDP, da Bashir Usman Tofa na jam’iyyar National Republican Convention NRC suka yi.

Babangida ya kuma bayyana nadamar shi, tare da kuskuren da ya yi, akan alhakin matakin da ya dauka, kuma hakan ya faru ne a karkashina a lokacin mulkinsa.

Acewarsa a lokacin sun fahimci hatsarin mika mulki ga gwamnatin farar hula, inda suka yi tunanin cewa matukar suka mika muli cikin watanni shida, za a kuma yin wani juyin mulkin wanda hakan zai kuma zama gazawa a bangarensu.

Babangida ya ce bayan soke zaben da yayi, gwamnatinsa ta shirya gudanar da wani sabon zabe a watan Nuwamban shekarar 1993, Amma bisa rikicin da ya biyo bayan soke zaben ba a samu damar yin wani zaɓen ba, kuma bisa haka suka kafa gwamnatin rikon kwarya, inda kuma daga baya Janar Sani Abacha ya kifar da ita.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: