Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Sulaiman Othman Hunkuyi a matsayin wakilin Arewa maso Yammacin Kasar nan a Hukumar Ayyukan Majalisar Tarayyar Kasar NASC.

Mai bai’wa shugaban Kasa Shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Dada Olusegun mai bai’wa shugaban kasa Shawara na musamman kan sadarwa da ya fitar a yau Alhamis.
Hunkuyi wanda ya kasance tsohon Sanata a Jihar Kaduna, Nadin nashi na zuwa ne Kwanaki Biyar da komawarsa jam’iyyar ta APC.

Hunkuyi wanda ya rike mukamin sanatan Kaduna ta Arewa a shekarar 2015 zuwa 2019 a jam’iyyar APC kafin sauya shekarsa zuwa wata jam’iyyar.

Shugaban ya nada Hunkuyi ne tare da wasu mutane, inda kowanne su zai gudanar da aiki a bangarori daban-daban.