Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a Jihar Legas ta bayar da umarnin karbe dala miliyan 4.7, da Naira miliyan 830, da wasu kadarori masu yawa da ke da alaka da tsohon gwamnan babban bankin Kasa na CBN Godwin Emefiele.

Alkalin kotun Mai shari’a Yellim Bogoro ne ya yanke hukunci a zaman kotun na yau Juma’a, bayan amincewa da rokon Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC wadda lauya Bilkisu Bala ta wakilta.

Kudaden da kotun ta bayar da umarnin kwace su na cikin asusun bankunan First Bank, Zenith Bank, Titan Bank, da wasu mutane da kamfanoni ke kula da su.

Daga cikin Kamfanonin sun hada da Omoile Anita Joy, da Deep Blue Energy Service Limited, Exactquote Bureau De Change Ltd, Kamfanin Lipam Investment Services Limited, Tatler Services Limited, Rosajul Global Resources Ltd, da kuma TIL Communication Nigeria Ltd.

Kadarorin da kotun ta bayar da umarnin karbe su na wucin gadi sun hada da Dakuna 94 na wani bene mai hawa 11 da ake ginawa a 2 Otunba Elegushi 2nd Avenue, Ikoyi Legas, AM Plaza, ofisoshi masu hawa 11 a ginin Otunba Adedoyin Grescent, Lekki Peninsula Scheme 1, a Jihar Legas, Imore Industrial Park a Esa Street, Imoore Land, a Karamar hukuma Amuwo Odofin a Jihar ta Legas da dai sauransu.

Alkalin kotun ya bayyana cewa dukkan kadarori da kudade an mallakesu ne ta haramtacciyar hanya, inda ya ce ya zama wajibi a mikasu ga gwamnati.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: