Majalisar Wakilan Najeriya ta hannun kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin Kasa na shekarar 1999 yaki amincewa da batun kirkiro da sabbin Jihohi 31 a Kasar.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Jihar Akwa Ibom a yau Juma’a.

Kalu ya bayyana cewa bukatar kirkiro da sabbin Jihohi da aka gabatar a gaban Majalisar ba su cika sharuddan kundin tsarin Mulkin Najeriya ba.

Taron wanda aka fara daga 20 zuwa 23 ga watan Fabrairun nan, inda aka shirya shirya taron don ‘yan kwamitin yiwa kundin tsarin mulkin Kasar garanbawul.

Majalisar ta shirya taron ne tare da hadin gwiwar cibiyar tsare-tsaren doka da kuma goyon bayan UK Foreign, Commonwealth and Development da ofishin FCDO.

Kalu ya kara da ce bukatar kirkiro sababbin jihohi na da matukar muhimmanci a tsarin mulki, kuma hakan yana haska burin al’ummomi daban-daban, inda ya ce bukatar samar da karin jihohi da aka gabatarwa Majalisar ba su cika dukkan sharruddan da doka ta tana da ba.

Kalu ya ce hakan ya sanya kwamitin ya kara wa’adin gabatar da bukatu akan gyaran kundin tsarin mulkin zuwa ranar 5 ga wata Maris din shekarar nan, don kara bai’wa mutane damar bayar da ta su gudummuwa akai.

Acewarsa za a iya ƙara wa’adin a nan gaba matukar kwamitin ya ga bukatar hakan bayan kammala tattaunawa a gurin taron, inda ya ce majalisar na kuma duba kudurori 151 na gyaran kundin tsarin mulkin Kasar, wanda hakan ke nuna kokarin ‘yan majalisar na kyautata tafiyar da tsarin mulkin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: