Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC, ta yi gargaɗi ga ɗalibai akan illar shaye-shayen ƙwayoyi da kuma sauran kayan maye.

Babbar daraktar hukumar Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗin a jiya Asabar, yayin wani jawabi na musamman a taron wayar da kai da aka shirya ga ɗalibai na matakin makarantun sikandire.
Adeyeye wacce ta samu wakilcin babbar jami’a a hukumar Harirah Abdullahi, ta ƙarfafi muhimmancin ƙudurin tare da bayyana matakin da shan miyagun ƙwayoyi ya kai a tsakanin matasan ƙasar nan.

Shirin dai ya gudana ne a makarantar sikandiren gwamnati ta Kamfanin Bobi, da kuma makarantar sikandire ta Mu’azu Ibrahim da ke Kontagora.

Adeyeye ta bayyana cewa babban ƙudurin tsarin shi ne don ilimantar da ɗalibai game da illolin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma haskaka muhimmancin zama cikin ƙoshin lafiya.
Ta kuma ƙara da cewa kimanin kaso 14.4 cikin 100 ko kuma mutane miliyan 14.3 na ƴan Najeriya sun afka matsalar ta shan miyagun ƙwayoyi, tare da bayyana cewa wannan gagarumar matsala ce da ta ke buƙatar kulawa ta musamman.
A nasu bangaren shugabannin makarantun sikandiren guda biyu, Mohammed Bagobin da Muhammad Nayawo sun godewa hukumar ta NAFDAC bisa zaɓo makarantunsu don gudanar da wannan ƙudurin, tare da kuma kiransu ga ɗaliban da su kula sosai akan abinda aka ilimantar da su akai.