Shugaban asusun tallafawa manyan makarantu TETFund Sonny Echono, ya buƙaci gwamnatin tarayya da na jihohi da su bai wa jami’o’i damar cin gashin kansu.

Echono ya yi wannan kiran ne jiya Asabar, a wajen wani taro mai taken “cin gashin kan jami’a da kuma ƙalubalen nagartaccen ilimi a manyan makarantun Najeriya”, wanda ya guda a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Oye-Ekiti.

Ya bayyana cewa jami’o’i wani waje ne can ƙololuwa da su ke da muhimman abubuwa guda uku: koyarwa, bincike da kuma ayyukan al’umma, kuma hakan na buƙatar cin gashin kai don samun abinda ya dace.

Ya kuma bayyana cewa idan su na son yin abinda ake buƙata, sai sun samu cikakken iko a jami’o’in gwamnatin tarayya da na jihohi gaba ɗaya, don samun cikakken ƴanci.

Ya kuma bayyana cewa cin gashin kai yana baiwa jami’a damar ta gina kanta, bunƙasa da samar da kayan aiki, da kuma haɗin guiwa da ƙasashen duniya, dan samun ingantaccen tsarin koyarwa da kuma binciken ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: