Jami’an Sojojin Saman Najeriya na Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka wasu manyan jagororin ’yan bindiga biyu a wani hari da suka kai musu ta sama a Jihar Katsina.

Wadanda aka hallaka sun hada da Gero Alhaji da Alhaji Riga, tare da yaransu fiye da 20 a wani daji da ke cikin karamar hukumar Faskari ta Jihar.
Jami’an sun kai harin ne a ranar Larabar da ta gabata, bayan samu bayanan sirri da suka yi akan maboyar ‘yan ta’addan.

Mataimakin mai magana da yawun Rundunar Kaftin Kabiru Ali, ya bayyana cewa jami’an sun kuma lalata maboyar ‘yan ta’addan, inda ya ce manyan ‘yan ta’addan biyu da aka hallaka sun kware wajen bai’wa ‘yan bindiga maboya, ya yin da suke yawan kaiwa matafiya hare-hare akan titin Funtua zuwa Gusau.

Acewarsa Jami’an sojin sama tare da hadin gwiwar Jami’an sojin Kasa za su tabbatar da ganin sun ci gaba da kai sumame sansanonin ‘yan ta’adda, don ganin an kawo karshen su.