Jami’an tsaro a Jihar Katsina sun samu nasarar kubtar da wasu mutane biyar da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Litinin.
Wasu majiyoyi sun ce maharan sun shiga Kauyen Kutungubus da ke cikin karamar hukumar Kankara da misalin ƙarfe 5:30 na asubahin jiya Lahadi, ina suka yi garkuwa da wasu mutane da ba kididdige adadinsu ba.

Makama ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaron soji hadin gwiwa da na ‘yan sanda da na sa-kai suka nufi yankin cikin gaggawa tare da rufe hanyar da ‘yan bindigan za su tsere da mutane a Mararraba Gurbi.

Bayan tsare hanyar jami’an tsaron sun yi musayar wuta da maharan wanda hakan ta tilasta musu tserewa, wanda hakan ya bai’wa jami’an tsaron damar kubtar da mutanen.
Mutanen da aka kubtar sun hada da Lamunde Musa, Nafisa Isa, Umma Tanimu, Hauwau Sani da kuma Halisa Sani.
Amma sai dai ‘yan bindigan sun tsere da wasu mutanen uku da suka hadar da Ayuba Ibrahim, Fariza Harisu, da kuma Guje Salihu.
Bugu da kari kuma da misalin karfe 10:30 na daren ranar wasu ‘ƴan bindigan sun kai hari Kauyen Dungum Sambo da ke a karamar hukumar Dandume.
Inda a nan ma jami’an tsaro suka gagauta zuwa yankin suka yi musayar wuta da maharan, har ta kai ga sun tsere dauke da raunuka a tare da su.
