Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta kammala dukkan shirinta na daukar matasa 10,000 aiki a ma’aikatu daban-daban na fadin Jihar.

Shugaban Ma’aikatan Jihar Barista Mohammed Sani Umar ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai wata ziyara Hukumar Kula da Harkokin Ma’aikata ta Jihar.

Mohammed ya ce shirin daukar matasan aiki zai taimaka matuka waje cike dukkan gurbin aiki a ma’aikatun gwamnatin Jihar da kuma guraren da ke bukatar karin ma’aikata.

Shugaban Ma’aikatan na Bauchi ya ce shirin zai kuma rage matsalar rashin aikin yi da zaman kashe wando da ya addabi matasa, wanda hakan zai ƙara inganta ayyukan gwamnatin Jihar.

Har ila yau ya bayyana cewa shirin daukar aiki da gwamnatin Jihar za ta yi na zuwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban hukumar Kula da Harkokin Ma’aikata a Jihar zai fara aiki.

Shugaban ya ce gwamnatin Jihar za ta bude shafin daukar aikin ta shafin yanar gizo domin cike takardar neman aiki cikin sauƙi, bayan amincewar gwamnan Jihar Bala Mohammed.

Acewarsa za su yi kyakkyawan shiri na musamman domin wayar da kan matasa domin sanar da matasa hanyoyin da za su bi wajen cike takardar neman aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: