Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa mulkin dimokuradiyya a nahiyar Afrika ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a birnin tarayya Abuja a gurin bikin cikar tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon gwamnan Jihar Imo Emeka Ihedioha shekaru 60 da haihuwa.
Acewara Obasanjo tsarin ya gaza samu ne sakamakom tsarin da ya ke kai bai yi daidai da al’adu ba, da kuma yadda rayuwa ke tafiya da a nahiyar, tare da wasu abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da akansu ba.

Tsohon shugaban ya yi misali da yadda tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln ya tabbatar da tsarin dimokuraɗiyya da bayyana cewa gwamnati ce ta al’umma da al’umma ke jagorantar ta domin mutane.

Acewarsa tsari ana yin shi ne domin amfanin kowa, ba sai wani bangaren na al’umma ba ko wasu kebantattun mutane ba.
Obasanjo ya kara da cewa kafin zuwan dimokuraɗiyyar Kasashen yamma, nahiyar Afirka na da nata tsarin shugabancin wanda ke kula da bukatun kowa, yana mai cewa wannan tsarin shi ne dimokuraɗiyya, ba wanda ake kira da dimokuradiyya ba a yanzu, da ke bai’wa shugabanni damar karbar duk abin da suke so ba bisa ƙa’ida ba ta hanyar cin hanci da rashawa, tare da bukatar mutane da su je kotu idan su na da shakku akai.
Acewarsa matukar ba a canja tsarin dimkuradiyya ba ta yi daidai da manufofin ’yan Afirka ba, to za ta ci gaba da durkushewa, wanda hakan zai kai ta ga mutuwa a nahiyar ta Afrika.
