Aƙalla gidaje 50 ne su ka rushe sakamakon wata gagarumar iska mai ƙarfi da ta auku a daren ranar Juma’a, a yankin Mahanga da ke ƙaramar hukumar Awe a jihar Nasarawa.

Ɗaya daga cikin jagororin yankin James Arthur ne ya bayyana hakan ga ƴan jarida a birnin Lafia, babban birnin jihar a yau Asabar.
Ya kuma roƙi gwamnan jihar Abdullahi Sule da shugaban ƙaramar hukumar da sauran ƴan siyasa, da su kawo ɗaukin gaggawa ga al’ummar da lamarin ya shafa.

Ya ce gagarumar iskar ta lalata musu gidaje, makarantu da sauran gine-gine, inda ta bar su cikin matsanancin neman taimako.

James ya ce kawo ɗaukin na hukumomi da sauran ƴan siyasa zai yi matuƙar taimaka musu, ta hanyar samar musu da kayan rage raɗaɗi kamar muhalli, da kuma taimaka musu.
Ya ce sama da gidaje 50 ne su ka rushe sakamakon iskar, inda ta yaye rufin gidajen da kuma rushe wasu, tare da barin su baki a buɗe.