Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta ce zuwa yanzu mutane 150 ne su ka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Niger.

Mai magana da yawun hukumar Ibahim Husseini ne ya bayyana haka wanda ya ce adadin ya karu daga 115 zuwa 150.


Sannan akwai wasu mutane 3,000 da ruwan ya salwantar da matsugunansu.
Gidaje sama da 250 ne su ka rushe a sanadin ambaliyar ruwan.
Bayanan na zuwa ne bayan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar da ta yi wani abu a kai.
Wasu gawarwakin da aka gano gidaje ne su ka dannesu bayan sun rushe.
Sai dai kuma har yanzu ana ci gaba da aikin ceto mutanen da ba a gani ba.
Wani ruwan sama da aka yi ranar Laraba ne ya yi sanadin ambaliyar a wasu unguwanni da ke ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja.