Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya musanta jita-jitar da ke yawo ce akwai rashin jituwa tsakaninsa da Mataimakinsa Yakubu Garba.

Gwamna Umar Bago ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan karbar lambar yabo daga ƙungiyoyin kwadago a gurin bikin ranar ma’aikata ta 2025 da aka gudanar a garin Minna babban birnin Jihar.

Gwamnan ya ce babu gaskiya a cikin jita-jitar, yana mai cewa akwai kyakkyawar alaka tsakaninsa da Mataimakin nasa.

Kazalika gwamnan ya ce mataimakin nasa bai samu damar halartar taron ba ne sakamakon wasu muhimman ayyukan da suka riƙeshi.

Acewar Bago sun kasance tsintsiya maɗauri daya tsakaninsa da Mataimakin nasa, kuma a halin yanzu sun mayar da hankali ne wajen ganin sun gina sabuwar Jihar Neja.

Bago ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da bata da tushe balle Makama.

A yayin taron gwamna ya samu rakiyar Sanata Mohammed Sani Musa mai wakiltar yankin Neja ta Gabas a Majalisar Dattawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: