Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya ce zai tabbatar dukkan sauye-sauyen da aka samu a dokar zaɓe sun kammala tsaf kafin zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Yakubu ya bayyana haka ne a jiya Litinin a fadar shugaban ƙasa.

Sannan ya musanta labaran da ake yaɗawa cewar an saukeshi daga shugabancin hukuma, wanda ya jaddada cewar har yanzu shi ne dai shugaban hukumar a Najeriya.

Wannan bayanai na zuwa ne yayin amsa tambayoyi daga yan jarida bayan bayan shaida naɗa wasu kwamishinonin hukumar biyu da shugaba Bola Tinubu ya yi a jiya.

Daga bibiyan da su ka yi dangane da zaɓen shekarar 2023 da ta gabata, sun gano abubuwa 142 kuma daga ciki akwai guda takwas da ke buƙatar sauye-sauye.

Mahmud Yakubu ya ce zai tabbata dukkan gyare-gyaren da ake buƙata a hukumar zaɓen an tabbatar da su kafin babban zaɓen da ke tafe

Leave a Reply

%d bloggers like this: