Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kaddamar da sabbin jiragen yaki biyi ga rundunar sojin saman Najeriya.

Shugaban ya kaddamar da jiragen ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda ilbikin ya kasance wani sashi na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya.
Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya wakilci shugaba Tinubu a yayin taron, inda ya bayyana cewa Kasa Najeriya na buƙatar tsaro mai inganci, don ganin ’yan Najeriya, sun samu damar yin rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Acewarsa ya zama wajibi a tabbatar da ganin an kawo karshen makiya Najeriya, ta hanyar samar da tsaro mai inganci.

Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba wajen ci gaba da sabunta kayan aikin sojojin Kasar, da kuma sanya hannun jari a fannin tsaro don tunkarar matsalar ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro a fadin Kasar.
Shugaban ya buƙaci sojojin da su ƙara kaimi a yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da su a Kasar nan, yana mai cewa zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da kuma ci gaban tattalin arziƙi sun dogara ne ga tsaron ƙasa.
