
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana irin Nasarori da Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta cimma a fannin tsaro cikin shekaru 2.

Ribadu ya gabatar da jawabin ne a yayin babban taron Jam’iyyar APC da ya gabata a ranar Alhamis a babban dakin Taro na Banquet Hall dake fadar shugaban Kasa.

Ribadu ya bayyana cewa kafin zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu, Najeriya na fuskantar manyan matsaloli guda biyar da suka haɗa da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma, rikicin ’yan aware a Kudu maso Gabas, rikicin manoma da makiyaya a Arewa ta Tsakiya da rikicin Neja Delta.
Ya bayyana cewa, matakan dakile wannan matsaloli da gwamnatin Tinubu ta dauka a shekara biyu ya samar da gagarumar nasara musamman a Arewa maso Yamma inda aka kuɓutar da mutane fiye da 11,000 da aka yi garkuwa da su.
“An yi nasarar hallaka shugabannin ‘yan bindiga kamar su Ali Kachalla, Boderi da Halilu Sububu, yayin da wasu 35 suka mika wuya karkashin shirin sulhu na “Kaduna Model.”
“A Arewa maso Gabas, fiye da ‘yan ta’adda 13,543 sun mutu tun bayan zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu. Fiye da 124,000 daga cikin mayakan Boko Haram da iyalansu sun mika wuya, an kuma kwato bindigu da alburusai masu tarin yawa a Jihar Borno.”
“A Neja Delta, an dakatar da satar danyen mai da rushe fiye da matatar mai wanda akai ba bisa ƙa’ida ba har 1,900 da wuraren hakowɗ mai 3,800. Samar da tsaro a yankin ya taimaka wajen samun ƙaruwar danyen mai da ake fitarwa daga kasar daga ganga miliyan 1 zuwa kusan ganga miliyan 1.8 a kullum.”
“A Kudu maso Gabas kuwa, ƙalubalen takunkumin zaman gida na dole da kungiyar IPOB ke tilastawa ya fara dusashewa, ofisoshin ‘yan sanda da dama sun koma aiki, kuma ana cigana da harkokin kasuwanci a yankin.” inji shi.
A ƙarshe, ya bayyana cewa, “Tsaro aikin ne na kowa,” yana mai kira da haɗin kai tsakanin dukkan matakan gwamnati da hukumomin tsaro domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya. Ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu bisa jagoranci mai kyau da umarnin da ya bayar tun farko, wanda ya bai wa jami’an tsaro dama su aiwatar da ayyukansu da kwarewa da kwazo.
