Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis mai zuwa 12 ga watan nan na Yuni da muke ciki a matsayin ranar hutu bisa zargayowar ranar Dimkradiyya ta shekarar 2025.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya tabbatar da hakan a yau Lahadi ta cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida Magdalene Ajani ta fitar.
Sanarwar ta ce Ministan ya taya al’ummar Najeriya murnar cika shekaru 26 da fara mulkin dimkradiyya a Ƙasar.

Ministan ya ce a kowacce ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ta kasance rana mai dumbun tarihi ga Najeriya.

Acewar sanarwar dimkradiyyar Najeriya ta samar da kasa mai gaskiya da adalci, yayin da zaman lafiya zai tabbata, makomar al’umma ta kasance cikin kwanciyar hankali.
Ministan ya yi kira ga ga ƴan Kasar nan da su ci gaba da goyon bayan dimokuraɗiyya, da zaman lafiya, haɗin kai, domin ganin Najeriya ta ci gaba da samun nasarori.