Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya bai’wa ƴan Kasuwar Kara bangaren ƴan Katako tallafin naira miliyan Goma domin rage musu radadin konewar shagunansu a lokacin da gobara ta tashi a Kasuwar.

Sannan kuma gwamnan ya jajantawa ƴan Kasuwar bisa asarar da suka tafka a yayin gobarar.
Gobarar ta tashi ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta haifar da asarar dukiya mai yawa a Kasuwar.

Gwamnan Nasir wanda mataimakinsa Umar Abubakar Tafida ya wakilta a ziyarar jaje da ya kai ’yan kasuwar.

Tafida ya ce tallafin shi ne na farko don ganin ƴan Kasuwar sun rage radadin halin da suke ciki.
A yayin ziyarar mataimakin gwamnan ya zagaya lungu da sako na Ƙasuwar domin ganin irin barnar da gobarar ta yi, inda ya ce gwamnatin Jihar za ta tabbatar da ganin ta tallafawa ƴan Kasuwar domin ganin sun ci gaba da gudanar da harkokin Kasuwancin bayan kammala ɗaukar dukkan bayanan da suka kamata na kasuwar.