Tsohon ministan Matasa da Wasanni Solomon Dalung bayyana cewa shekaru biyu da shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kwace akan karagal mulkin Najeriya su ne shekaru mafi muni a Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Dalung ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC kan batun ranar Dimkradiyya a Najeriya, yana mai cewa ko kadan talakan Najeriya bai amfana da roman dimkuraɗiyya ba daga gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Tsohon Ministan ya kara da cewa tun bayan hawan gwamnatin shugaba Tinubu abinda ɗan Najeriya ƙadai ya samu daga gwamnatin shine tsadar rayuwa, Talauci, rashin tsaro, yunwa da kuma shiga halin kuncin rayuwa.

Dalung ya kuma nuna takaicinsa kan cire tallafin man fetur, inda ya ce cire tallafin man ba tare da yin wani shiri da zai hana ƴan Ƙasa fadawa cikin wani hali hakan ya jefa da yawa daga cikin ƴan Ƙasa cikin halin kuncin rayuwa.

Acewarsa a halin yanzu Dimkuradiyyar Najeriya ta cikin mawuyacin hali tun bayan hawa shugaba Tinubu kan mulki.
A jiya Alhamis 12 ga watan nan na Yuni da muke ciki ne aka gudanar da bikin ranar Dimkradiyya a Najeriya ta cika shekaru 26 da dawowar mulkin Dimkrɗiyyar.
To sai dai a bikin na bana ƴan Ƙasar da sauran ƴan siyasa har yanzu kowa yana tofa albarkacin bakinsa kan ci gaban da aka samu tun bayan dawowar mulkin na Dimradiyya a Najeriya.