Rundunar ƴan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da kubtar da wasu mutane 73 da aka yi garkuwa da su a wasu sassan Jihar.

Sannan kuma rundunar ta kama mutane 175 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Abubakar Sadik Aliyu ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.

Rundunar ta ce nasarar ta samu ne a cikin watan Mayun da ya gabata.

Sanarwar ta ce daga cikin mutanen da aka kama cika harda mutane 15 da ake zargi da hannu a aikata ayyukan fashi da makami.

Sauran sun hada da wani mutum guda da ya mallaki bindiga ba bisa ƙa’ida ba, da wasu mutane 20 da laifin kisan kai da wani mutum guda da laifin garkuwa, da kuma wasu mutane 30 da laifin aikata fyade, sannan kuma mutane 108 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Kakakin ya kuma ce jami’an rundunar sun kuma kwato bindigogi kirar gida, da harsasai 506, babura biyu, da kuma dabbobin sata 174.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: