Jami’an sojin Najeriya sun hallaka wasu shugabannin ƴan ta’adda shida, tare da karin wasu goma a Jihar Zamfara.

Nasara ta samu ne a gurare daban-daban daga jami’an Mobile Strike Team da ke ƙarƙashin Operation Fansan Yamma a wani sumame da suka kai.
A cikin sanarwar daraktan hedkwatar tsaro ta Ƙasa Manjo Janar Markus Kengye ta fitar a jiya Alhamis,yta ce Jami’an sun samu nasarar ne a wani samame da suka kai garin Kunchin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar.

Ya ce jami’an sun samu nasara ne a ranar 10 ga watan nan na Yuni da muke ciki.

‘Yan ta’addan da aka hallaka sun hada da Abdul Jamilu, Salisu Auta, Sale Ado Madele wanda ya kasance ɗa ga Ado Aliero, Babaye da kuma wani da a bayyana sunan shi ba.