Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana damuwa matuka kan rikicin da ke kara kamari tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Kasar Isra’ila, inda ta yi Allah-wadai da harin farko da Isra’ila ta kai kan Iran, wanda ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici mai hatsari.

Najeriya ta yi kira da a dakatar da harin tare da kira ga bangarorin biyu da su nuna juriya da hakuri don kare zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya. Ta bayyana cewa, ci gaba da mayar da martani tsakanin kasashen biyu zai cigaba da barazana ga rayukan fararen hula da kuma kara tayar da hankalin duniya, ciki har da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro.
A cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar daga birnin Abuja a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2025, Najeriya ta bayyana cewa tana tsaye tsayin daka kan bin ka’idojin zaman lafiya da amfani da hanyar diflomasiyya wajen magance wannan rikici.

“Najeriya na kira ga kasashen biyu da su zabi tattaunawa maimakon fada. Haka kuma, muna kira ga al’ummar duniya musamman Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su kara matsa lamba domin ganin an samu saukin lamarin da kuma samar da yanayi na shawarwari masu amfani,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa yaki ba zai iya maye gurbin sulhu ba, sannan mafita mai dorewa tana cikin tattaunawa, mutunta juna da bin dokokin kasa da kasa. Najeriya ta ce a shirye take ta goyi bayan duk wani yunkuri na gaske da zai taimaka wajen rage tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.