Hayaniya ta ɓarke bayan da shugaban jam’iyyar APC na shiyyar arewa maso gabas ya ayyana amincewa da tazarcen shugaba Tinubu ba yare da Kashim Shettima ba.

Wani biidiyo da yake yawo a kafofin sa da zumunta an hango jami’an tsaro na fita da shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Ganduje.

Taron wanda aka yi a jihar Gombe, ya samu halartar ministoci, da gwamnoni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na shiyyar.

Yayin da shugaban jam’iyyar na shiyyar arewa maso gabas Mustapha Salihu ke bayani ya ƙi ambatar sunan Kashim Shettima bayan da ya ayyana Tinubu a matsayin wanda su ke goyon bayan sake fitowarsa takara a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Lamarin da ya haifar da hayaniya.

Haka zalika Ganduje bai ambaci sunan Kashim a yayin da yake nasa jawabin ba

Batun da ake zargin akwai lauje cikin naɗi.

Ba tun yanzu ba ake zargin akwai saɓni tsakanin shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima batun da ake ta musantawa.

Ana zargin shugaba Tinubu na iya ajiye Kashin tare da ɗakko sabon mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: