Mutane 11 ne su ka rasu sakamakon fashewar nakiya a jihar Borno.

Lamarin ya faru a ƙaramar hukumar Kondugaa jihar jiya Juma’a da daddare.

Nakiyar ta fashe a kusa da wani gidan kallo da ke gefen kasuwar kifi ta Konduga.

Rundunar yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin yau Asabar.

A cewar mai magana da yawun yan sanda Kenneth Daso, mutane 10 ne su k mutu yayin da wasu d dama su ka jikkata.

A gefe guda kuwa ana zargin mutanen da su ka mutu sun kai 20.

A cewarsa wata mace ce yar kunar bakin wake ta tashi abin fashewar da ƙarfe 10pm na daren jiya Juma’a.

Tuni jami’an tsaro su ka isa wajen don tabbatar da komai ya daidaita tare da komawa ci gaba da al’amuran yau da kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: