
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa ayarin masu zuwa biki mutum 12 a jihar Filato, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin ƙyama da rashin imani.

A cewar sanarwar da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Lahadi, Shugaba Tinubu ya umarci rundunar ƴan sanda ta ƙasa da su haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri don gano waɗanda suka aikata wannan ta’asa tare da hukunta su.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka kashe da waɗanda suka ji raunuka sun taho ne daga Zaria zuwa Jos don halartar bikin aure inda ’yan ta’addan suka rutsa su suka kashe su.
Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa ba za a lamunci zubar da jinin mutane ba gaira ba dalili, yana mai kira ga gwamnatin Jihar Filato ta ɗauki matakin gaggawa don dakile irin wannan mummunan al’amari.
“’Yancin zirga-zirga ga kowane ɗan ƙasa abu ne da ba za a iya kawo masa tsaiko ba. Ba za mu yarda wani ko wata ƙungiya ta hana hakan ta hanyar amfani da tashin hankali da firgita jama’a ba,” in ji Shugaban Ƙasa.
Shugaba Tinubu ya kuma mika ta’aziyya da jaje ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su da kuma gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan babban rashi.
Shugaban ƙasar ya yi alwashin cewa ba za a bar wannan kisan ya tafi a banza ba, za a tabbatar da cewa an yi ma masu hannu a ciki hukunci. Ya kara da cewa dole ne a kawo ƙarshen wannan zubar da jini da ke ci gaba da dagula zaman lafiya a yankunan ƙasar.