Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba

Taron karawa juna sani na Malaman Makarantun Allo na Kaura-Namoda da kewaye na wuni biyu, wanda Ƙungiyar Sawabiqul Jiyadi ta shirya a ranakun Assabar da Lahadi an gabatar da Maƙaloli kamar haka:

A rana ta farko Malam Falalu Mahi Kamarawa ya gabatar da takarda mai taken *Rawar da Makarantun Allo ke takawa wajan kyautata tarbiyyar Al’umma.* Yayinda Sheikh Malam Junaidu Usman Limamin Masallacin Juma’a na Sheikh Isa Bini Ramadan Lugun Malamai yayi mata ta’aliki.

Shima Malam Shehu Salisu Na ‘yan Zikiri ya gabatar da tasa mai taken *TsaraTsaren da Makarantun Allo ya kamata su bi wajen karbar Dalibai da samar masu da isasshen wurin kwana.*
Yayinda Farfesa Jafaru M. Kaura yayi mata ta’aliki.

A rana ta biyu an gabatar da Makala daya mai taken *Samarwa Dalibai hanyoyin Dogaro da kai*, wadda Malam Kabiru Usman Sama’ila (Dan-Kabi) ya gabatar, yayinda Dakta Aminu Umar Gummi sakataren zartarwa na hukumar bunkasa ilimin harshen Larabci da addinin musulunci na jaha yayi masa ta’aliƙi.

An karama sama da mutane 400 da takardar shedar halartar taron da kuma wasu daga cikin wadanda suke baiwa wannan ƙungiyar goyon baya da hadin kai.

Shima a nasa jawabi Shugaban Kungiyar Alh Jalaluddeen Sambo ya yi Godiya ga dukkanin wadannan suka halarci wannan taro inda yace ayyukan wannan ƙungiya zasu cigaba a kowane yanki daya shafi addini kamar yanda aka sani babu inda sukafi maida hankali kamar sha’aninda ya shafi Addinin Musulunci.

ya ci gaba da cewa wannan ƙungiya ta kafa makarantun addini sama da ƙirgawa sannan dukkanin makarantun dake wannan yanki na islamiyya da kulliya yana da wahala a rasa wakilan wannan ƙungiya daga cikin jagororinta, sunnan wanna kungiya batada alaƙa da kowane Dan siyasa ko Gwamnati, kuma gudummawarsu tana kaiwa har gidajen gyaran hali da Assibitocin wannan yanki.

  1. Manyan mutanen dama sun sami halarta a wadannan ranakun ciki har da Dr Yusuf Nasir Tsohon shugaban Makarantar Federal Polytechnic kaura, Babban limamin masallacin juma’a na biyu Malam Badamasi Dalhatu, Khalifa Malam Maisuna na Malam Babba, Khalifa Malam Muhammad na gangaren Makaranta, Khalifa Malam Sani Malam Mahi Kamarawa Babban limamin masallacin Ƙadiriyya, Sakataren ilmi na Kaura Bashir Muhammad, Ibrahim Isah Daraktan Makarantun Allo na jaha, wakilin Uban kasar barayar zaki da dukkanin jagororin Kungiyar da yan kwamiti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: