Daga Abba Anwar

Ta kowace fuska ka kalli yadda yanayin siyasar Kano ke juyawa, dole mutum ya kara sakankancewa da cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, kuma Mataimaki na Farko ga Kakakin Majalisar Kungiyar Cigaban Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS Parliament), wato Sanata Barau Jibrin, ya zama mutum mai fada a ji a wannan jihar ta mu. Tare da kuma sakankancewar cewar Allah Ya sa shi cikin wadanda ke iya juya yanayin siyasar jihar


Ba tare da wata kambamawa ba, kowa ya san cewar wannan mutum ne mai hangen nesa, ga kamewa ga barin hayaniya irin ta siyasa kuma jagora ne na gari. Harkarsa ba hayaniya ba ji-ji-da-kai ba kuma dagawa. Sai tsantsar son a tallafi rayuwar al’umma. Mutum ne da ya san me yake. Kuma ya san mecece manufar da ya sa a gaba.
Shi a kullum babban burin sa shine ya ga ya zama sanadin samawa al’umma mafita ta hanyar ilmantarwa da kuma samun daidaito wajen neman ilimi. Shi ba dan hayaniya ba ne. Mutum ne kamilalle mai hangen nesa tare da daukar kowa a matsayin mutum mai ‘yanci ba bawa ba.
A takaicen takaitawa dai Sanata Barau ba shi da sa’a kakaf a jihar Kano wajen tallafawa harkar ilimi ga al’ummar mu, musamman matasan mu. A duk daidaikun yan siyasar mu. Ba wai ba inke! In gaya maka wani abin mamaki, ai ko gwamnatin jihar Kano mai ci a yanzu sai ta daga masa kafa wajen tallafawa dalibai a hanyar su ta neman ilimi. To balle kuma a ce wasu ‘yan siyasa daidaiku.
Shi fa ya yarda da cewar daga cikin manyan abubuwan da ke samawa dan Adam ciakken ‘yanci shine ilimi. Shi ya sa ba ya kasa a gwuiwa wajen ganin ya tallafawa al’ummar sa ta wannan hanyar.
Bari dai na yi wa mai karatu cikakken bayani, a gaba dayan Kano ta Arewa, wato bangaren da Sanata Barau yake wakilta a Majalisa, babu wani zababbe ko nadadde a can gwamnatin tarayya da ya isa ya gwada kwanji da Barau wajen tallafawa harkokin ilimi.
Wannan kuwa tun daga lokacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hau mukami kawo yanzu. Ai watakila ma tun kafin zuwan Tinubu. Wannan ban daukewa kowa ba. Dukkan zababbun da nadaddun da su ka fito daga wannan bangaren na Kano ta Arewa.
Wannan maganar tawa fa ina yi ne ga mutanen da su ka san ciwon kansu. Kuma suke da tunanin yi wa al’ummar su aiki. Ba ire-iren ‘yan son zuciya da nuna bakin cikin ba wani sai su ba. Ba ina nufin wadanda ke da muguwar cutar nan ta son kai mara kan gado ba.
Ina sanar da ko ma wanene da ya fito daga wannan bangaren na jiha, tsakanin zababbun da nadaddun da suke matakin gwamnatin tarayya, a nuna min wanda ya kai rabin rabin Sanata Barau wajen tallafawa al’umma kan harkar ilimi da ilmantarwa.
Bawan Allah kuma mutumin kirki Sanata Barau, shine wanda ya kai kuduri Majalisa har a ka kafa sabuwar jami’a a shiyyarsa bangaren Kabo. Wato Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kabo (Federal University of Science and Technology, Kabo).
Ya kuma dauki nauyin karo karatu ga matasan mu zuwa kasashen waje. Ya yi haka ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba. Lokacin da a ka fi ganin haka shine lokacin da ya dauki nauyin karatun matasa su Saba’in (70), zuwa kasashen waje dan karo karatun Digiri na Biyu, a fannonin ilimi na zamani. Irin bangarorin “Artificial Intelligence” da “Cybersecurity” da “Robotics Sciences” da dai sauran bangarorin da a ke alfahari da su yanzu a duniyar ilimi.
Sa’annan a cikin jam’i’o’inmu na gida kuma ya dauki nauyin karatun dalibai Dari Uku (300). Su ma dan ci gaba da karatun Digiri na Biyu, a manyan jam’i’o’i irin su BUK, ABU, University of Lagos, University of Ibadan da sauran su. Kuma su ma din sun dauki bangarorin karatu irin fannonin da a ke alfahari da su yanzu a duniya.
Dan dai mai karatu ya san da cewa, shi fa Sanata Barau, nasa ba irin nasu ba ne, ya dauki nauyin karatun dalibai sama da Dubu Biyu (2,000), dan karanta Digirin Farko a bangarorin karatu daban daban a shiyyoyin jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma da suke nan Kano. Wato “Learning Centres” na “Federal University, Dutsinma.”
Ai abin ba ma a nan kawai ya tsaya ba. Sanatan ne fa da kansa ya tsaya tsayin daka ya tabbatar an kawo “Learning Centres” din na jami’ar Dutsinma din, har guda 6 a nan Kano dan saukaka karatun ga dalibai. An samar a Gwarzo da Tofa da Bichi da Dawakin Tofa da kuma Dambatta. Baya ga tun da farko da a ka rigaya a ka samar ta cikin makarantar CAS Kano.
Daga wata majiya mai tushe daga jami’ar Dutsinma din an tabbatar min da cewa sama da kashi 98 cikin dari (98%) na daliban dake karatu a wadannan “Centres” din, Sanata Barau ke daukar nauyin karatun su. Idan har ba a jinjinawa wannan ba dan Allah wa za a jinjinawa a wannan bangaren haka? Wai me ya sa ne mutane ba su da tsinkaye?
Wani kuma babban abin bajinta da alfahari ga wannan Sanatan shine, tun ma kafin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya yi iya kokarin sa wajen ganin an bude Centres na National Open University of Nigeria (NOUN), a kowace karamar hukumar da take karkashin wakilcinsa. Wato a kananan hukumomi 13 dake a Kano ta Arewa.
Kuma a wadannan santocin ma ya dauki nauyin karatun dalibai dubunnai daga lokacin zuwa yanzu. Jagoranci kenan mara kyashin taimakon al’umma. Kullum babban burinsa shine ci gaban al’ummarsa. Ba ya daga cikin tsarin sa bautar da magoya baya. Kowane mutum a wajen sa “yantacce ne.
Shi fa Sanata Barau bai taba zama da takaitaccen tasiri na siyasa na nan-da-can ba. Ko a ce dan yanki kadan. Ko a ce daga nisan baki zuwa hanci. Abinda a turanci a ke cewa “Local Champion.” Kimarsa ta wuce nan. Kuma abin duk daga Allah ne. Ba tsiminsa ko dabararsa ta ba shi hakan ba.
Dan kuwa shi tasirin siyasarsa ta wuce iya kananan hukumomi guda 13 da yake wakita. Tasirin ga shi nan a Kano kowa na gani. Kamar yadda yake da tasirin siyasa a Arewa Maso Yamma. In takaicewa mai karatu bayani, Sanata Barau a kasashen Afirka ta Yamma a na jin amonsa. Kasancewarsa Mataimaki na Farko na Kakakin Majalisar Tarayyar Kasashen Afirka na Yamma, wato ECOWAS. Da kuma irin yadda yake kokari wajen tafiyar da Majalisar ta ECOWAS din.
Ai mun ga yadda kwanan nan ma wata gamammiyar kungiyar wasu matasa a Afirka ta Yamma su ka girmama shi kan yadda yake iya nasa kokarin wajen ganin an samu hadin kai mai dorewa da ci gaban al’umma a wadannan kasashe. Sun taso tun daga kasashen su musamman zuwa Najeriya dan su ba shi wannan lambar girma.
Har yanzu fa a tarihin siyasar jihar Kano a wadannan shekarun da muke ciki, ba wani ko wasu gungu na yan siyasa da za su hada kan su da shi ba wajen gano amfanin tallafawa al’umma bangaren da ya shafi ilimi. Har zuwa yanzu dai babu wannan. Ba a san ko nan gaba ba.
Ina shawartar yan siyasar mu da su dinga koyi da Sanata Barau wajen tallafawa harkokin ilimi. Haka kuma ina kara shawartar gwamnatin jihar Kano da kar su yi kasa a gwuiwa a wannan fannin. Kamar yadda Sanata ba ya yin kasa a gwuiwa.
Kuma shi da kansa ya sha bayyana irin yadda a kodayaushe yake ba harkar ilimi muhimmanci a rayuwa. Shi ya sa ma a ke ta ganin abubuwan alheri da yake yi wa jama’a wajen tallafawa harkokin su na karatu.
SHI DAI SANATA BARAU BA KANWAR LASA BA NE IN KA NA MAGANAR HIDIMTAWA JAMA’A.
Anwar ya yi wannan rubutun ne daga Kano
Laraba, 17 ga Satumba, 2025