Ba wai ba inke, ba kuma magana ce mara kan gado ba, idan a ka ce Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya kuma Mataimaki Na Farko na Kakakin Majalisar Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS Parliament), wato a Sanata Barau I. Jibrin, ba wai kawai ya ciri tuta ba ne wajen irin tallafin da yake ba bangaren ilimi ba, shi din jagora ne abin koyi a irin wannan hoɓɓasa.

 

Ya ciri tuta wajen tallafawa matasanmu da su samu ilimi nagartacce dan cigaban kansu da kuma al’ummar mu. Daga matakin jihar Kano har zuwa ga kasa gaba daya. Akwai tabbatattun bayanai da suke yun nuni ga hakan. A wajen sa ilimi shine mabudi.

 

Ba tare da wata ja-in-ja ba, mutum zai iya zuwa ire-iren manyan makarantun da Sanata ke daukar nauyin karatun dalibai zai kara samun cikakkun bayanai kan hakan. Akwai manyan makarantunmu da suke jihar Kano. Yadda Sanatan ke daukar nauyin daliban da su ka fito daga mazabarsa ta Kano ta Arewa.

 

Ga kuma manyan jami’o’in da ya kai dalibai ‘yan jihar Kano dan yin karatun Digiri na farko. Satuttukan baya ne ma a ka yi bikin tabbatar da dalibai su Dari Uku (300) da a ka tuttura manyan jami’o’ i dan yin karatun Digiri. Akwai makarantu irin su Bayero University, Kano, Amadu Bello University, Zaria, University of Lagos, Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, University of Ibadan, Federal University, Dutsinma, University of Nigeria, Nsukka da sauran manyan makarantu.

 

Wannan kuma fa ba a ma yi maganar dalibai guda Saba’in (70) da kwanan baya can ya tura su dan su yi karatun Digiri na Biyu a kasashen waje.

 

Daga cikin manyan dalilan da su ka sa Sanata Barau yake bayar da kulawa ta musamman ga bangaren ilimi shine, ya yarda cewar ilimi mabudin alhairai ne. Kuma wata hanya ce daga cikin hanyoyin ‘yantar da kai daga kangin bauta.

 

Akwai dalibai su Dubu Biyu (2,000) daga yankin sa na Kano Ta Arewa da ya sama musu gurbin karatu kuma ya dauki nauyin karatun su gaba daya a Federal University, Dutsinma. Dukkansu za su yi karatun Digiri na Daya.

 

Daga baya kuma ya kara fadada yawan daliban ya karo dalibai Dubu Daya (1,000) da a ka samo su daga Kano Ta Kudu da kuma Kano Ta Tsakiya. Ka ga ya game jihar kenan gaba daya.

 

Sune wadanda a cikin satin nan a ka je can harabar jami’ar ta Dutsinma a ka yi bikin shigar su makarantar. Wanda a wajen bikin wani kwamiti ne mai karfi ya wakilci Sanatan. A cikin tawagar akwai shugaban Hukumar Cigaban Yankin Arewa Maso Yamma, Farfasa Shehu Abdullahi Ma’aji, sai Mai Ba Sanatan Shawara kan Harkokin Mata, Hajiya ‘Yardada Maikano Bichi, akwai Shugaban Ma’ aikatan Ofis din Sanatan, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah da kuma daya daga cikin makusantan mataimaka na musamman da Sanatan, wato Shitu Madaki.

 

Sa’annan kuma duk a cikin satin nan da muke ciki, an yi bikin daukar nauyin dalibai guda Dubu Daya (1,000) a Bayero University, Kano, wadanda su ka fito daga Kano Ta Arewa, mazabar Sanatan. Duk an biya musu kudaden karatun, wanda kowannensu a ka biya masa sama da Naira Dubu Dari Takwas (800,000). Kwanan nan a ka yi bikin a BUK a idon kowa. Wanda Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya wakilci Sanata Barau a wajen bikin. Nan ma daya daga cikin masu hidimtawa Sanatan na kusa, wato Shitu Madaki ya halarci taron.

 

Ba ma wannan ba ma kawai, Sanata Barau ya na daukar nauyin karatun daliban da ke karatu a manyan makarantun jihar Kano, wadanda su ka fito daga mazabar sa ta Kano Ta Arewa. Bikin da a ka yi a BUK ai na su daliban da su ka fito daga mazabar tasa ne. Na samu labarin cewa za a ci gaba da irin wadannan bukukuwan a ragowar manyan makarantun Kano. Na ji an ce ba da dadewa ba za a ci gaba da Northwest University, Kano.

 

Kuma daga cikin ire-iren kwasa-kwasan da da a ke tura dalibai su karanta har da su Artifical Intelligence, Robotics Technology, Cybersecurity, Data Science, Information Technology, Software Engineering, Exploration, Hydrogeology and Environmental Geology, Oil and Gas Operations, Applied Geophysics, Climate Change Management, Metallurgical and Material Engineering, Mechatronics and Intelligence Systems.

 

Ni dai har yanzu, a daidaikun mutane dai, ban ga wanda yake wa ilimi hidima ba kamar yadda Sanata Barau yake yi. Ba ma fa a jihar Kano ba, a gaba dayan Arewa Maso Yamma. Ni dai ban gani ba.

 

Amma idan da akwai dan Allah a nuna min. Kuma a zo min da tabbataccen bayani kan hakan. Saboda shi duk abubuwan nan da na fada na irin hobbasarsa an yi a idon mutane an gani. Kuma an je har makarantun an yi bukukuwa kan hakan.

 

Da nake ganin irin wannan hobbasa ta Sanata sai kawai ya tuna min da lokacin da Kanar Sani Bello yake mulkin Kano a mulkin soja. Lokacin da ya kafa makarantun Dawakin Tofa Science Secondary School da Dawakin Kudu Science Secondary School. Wadannan makarantu sun yi tasiri sosai wajen samawa jihar Kano kwararrun likitoci da injiniyoyi masu inganci.

 

Ba na raba daya biyu, a yanzu a haka sama da kashi Saba’in cikin Dari (sama da 70%) na likitoci da injiniyoyi da muke da su, wanda wasunsu sun watsu cikin kasa da duniya, daga wadannan makarantun suke. To shi Sani Bello ya yi ne a matsayin gwamnati a lokacin.

 

Daga baya kuma a ka dinga samun sake daga bangaren gwamnatoci har kawo yanzu. Hakan ya sa a ka samu wani wawakeken gibi kan al’amarin harkar ilimi. To Sanata Barau ya zo ne dan ya cike wannan gibin. Da Yardar Allah.

 

Baya ga cewar har yanzu ni dai idona bai nuna min wani makamancin Barau ba a wannan fuskar. Kuma babban abin ban sha’awa shine, dukkan abubuwan nan da na fada za a iya ganinsu kuru – kuru idan a ka bincika hanyoyin zamani na samun labaran abubuwa. Irin su Google ko Chatgpt. Dan kuwa komai an yi shine a gaban jama’a a gaban ‘yan jarida kuma.

 

Sannan mutum na iya zuwa makarantun da na ambata a bisa ya binciki hukumomin makarantun kan yadda Sanatan yake daukar nauyin dalibai karatu a makarantun. Abin dai kawai a bude yake. Ba rufa-rufa.

 

Ni fa yadda nake kallon abin shine, nan da ‘yan shekaru kadan masu zuwa Kano za ta haifar da Kwararrun Masana na Sanata Barau, wanda a turanci na kira su da “Barau Scholars.”

 

Kuma fa su duk wadanda Sanatan yake daukar nauyi, sun fito ne daga jam’ iyyun siyasa mabanbanta, ba sai lallai ‘yan APC ba. Ya yarda kowa da kowa nasa ne, tun da shi shugaba ba ne. Ba ma maganar wai ‘yan wane bangare ne a cikin APC ba. An debo su daga dukkan sassan jihar. A wajen sa dukkan su ‘ya’yansa ne. Sanata kowa naka.

 

Kallon da kodayaushe nake yi wa Sanata Barau wajen kishin ilmantar da al’ umma shine irin kallon da nake wa Kanar Sani Bello da kuma marigayi tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano, Muhammadu Abubakar Rimi. Allah Ya jikansa da Rahama, ameen.

 

Abba Anwar ya rubuto wannan daga Kano

Asabar, 27 ga Satumba, 2025

Leave a Reply

%d bloggers like this: