Rahotanni daga helkwatar jam’iyyar APC a Abuja sun tabbatar da cewar har yanzu ba ta fara siyar da tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa da sauran madafun iko ba.

Jam’iyyar APC ta gamu da cikas kan shirinta na fara sayar da fom din takara domin darewa kujerun siyasa a zaben 2023 a ranar yau Asabar.
Masu neman darewa kan madafun iko a karkashin inuwar jam’iyyar a zaben 2023 dai sun yi cirko-cirko a hedikwtar jam’iyyar ta kasa, ganin cewa ba a fara sayar da takardun ba kamar yadda aka tsara.

Wata majiya mai tushe a jam’iyyar da ta nemi a boye sunanta ta ce, “Hakan ya faru ne saboda dan kwangilar da aka ba wa aikin buga takardun bai kawo su ba, watakila ya kawo kafin a gama hutun karshen mako.
Majiyar ta ce idan har hakan ta faru, za a iya fara sayar da fom daga ranar Litinin ko Talata.

Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na Kasa ne zai yanke shawara kan sabon lokacin da za a fara siyar da tikitin takarar.
Duk yunkurin jin ta bakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyar APC na Kasa, Felix Morka, bai amsa sakonnin da aka tura mishi ba.
Sannan jam’iyyar ba ta bayyana a hukumance dalilin da ya haifar da tsaiko wajen siyar da tikitin tsayawa takarar ba.