Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna Yekini Ayoku ya sha alwashin samar da sabbin dabarun aikin domin magance matsalar staro a Kaduna.

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin a ya kai ziyara fadar sarkin zazzau Ambasada Nuhu Ahmad Bamalli yau Litinin.
Ziyarar da sabon kwamishinan ƴans andan jihar ya kai fadar domin neman saka masa albarka bisa rakiyar wasu manyan jami’an ƴan sandan.

Kwamishinan ya tabbatarwa da masarauta da al’ummar Kaduna musamman yankunan da su ke fama da tashe-tashen hankula da cewar za a kawo karshen matsalar ba da jimawa ba.

Sabon kwamishinan ya ce zai yi amfani da sabbin dabarun aiki dn ganin an kawo ƙarshen matsalar da ake fuskanta ta hare-hare a faɗin jihar.
Sannan ya tabbatar da cewar za a ƙara yawan jami’an yan sanda domin gannin an tabbatar da tsaro a wuraren da su ke fama da matsalar tsaro.
A wani labarin kuma rundunar ƴan sanda a Kaduna ta kuɓutar da wata tankar mai maƙare da man fetur wanda wasu ɓarayi su ka yi awon gaba da ita.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Muhammaed Jalige ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.
Ya ce a kama mutane uku da ake zargi sun tafi da tankar mai wadda man fetur ɗin ciki ya haura naira miliyan shida.
Lamarin ya faru a ranar 16 ga watan Afrilun da mu ke cikin yayin da direban motar da yaronsa su ka ɗakko tankar man daga Legas zuwa Kaduna.
A binciken da ƴan sanda su ka gudanar sun gano cewar an raba man fetur ɗin a wasu gidajen mai guda biyu.
Muhammed Jalige ya ce su na kan gudanar da bincike domin samun cikakken bayani daga mutanen da su ka kama.