Ahmad Sulaiman Abdullahi

Dakarun sojojin Najeriyan sun samu nasarar halaka mayaƙan ta’addanci na Boko Haram da ISWAP da ke yankin Manjo Ali Ƙere a jihar Borno.
Cikin wani rahoto da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa dakarunta sun kai samamen yankin Manjo Ali Ƙere inda suka ragargaji ƴan ta’adda.

Cikin nasara da sojojin suka samu hada kwace miyagun makamai da suka haɗa da bindigogi da kuma harsasai masu yawa.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Afirilun 2022 inda sojojin suka sheke Amir da wani shugaban malaman ƴan ta’addan na Galta a samamen.
A hotunan da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter, an ga makamai da suka haɗa da bindigogi da harsasai wadanda sojojin suka yi nasarar kwacewa daga hannun ƴan ta’addan.