Gwamnatin Tarayya haɗin gwiwa da ƙungiyar kamfanonin sadarwa na duba yiwuwar kara farashin kiran waya da na data a Najeriya.

Cikin wata wasiƙa da haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa su ka aikewa hukumar sadarwa a Najeriya sun sanar da yiwuwar kara farashin kiran waya da na data da kuma kuɗin aika saƙon kar ta kwana na SMS.
Ƙungiyar ta ce ya zamar mata wajibi ta ƙara farashin duba ga hauhawar kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar.
Wasiƙar da su ka aike ta ce za a ƙara kiran waya daga naira 6.4 zuwa naira 8.95 a kowacce daƙiƙa, wanda ya kama naira 53.7 kowanne minti.

Shi kuwa saƙon kar ta kwana na SMS zai koma naira 5.61 maimakon naira 4 da yake a baya.

Farashin data kuwa zai koma naira 3200 maimakon naira 2800 da ya ke a baya.
Ƙarin farashin ka hau da kashi 40 cikin ɗari.
Kamfanonin sun ce, daukar wannan mataki ya zame musu dole duba da yadda suke fuskantar tsadar gudanar da harkokinsu a kasar.
ALTON ta ce kamfanonin sadarwar suna fuskantar kalubale sosai a Najeriya tun bayan bullar annobar COVID-19 a 2020 da kuma yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.
Kungiyar ta ce yakin Rasha da Ukraine ya sa kamfanonin fuskantar karin farashin man gas da suke amfani da shi da kashi 35 cikin 100.