Fadar shugaban ƙasa a Najeriya ta ce shugaba Muhammadu Buhari zai miƙa ragamar mulkin ƙasar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2923.

Hakan na ƙunshe a bayanin da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban zai miƙa mulkin domin tabbatar da demokaraɗiyyar ƙasa.
Saƙon mai kama da martani a kan ra’ayin ƴan kasar wanda aka jiyo wani babban lauya na faɗar cewar shugaban ya na da damar ƙara watanni shida bayan kammala zango na biyu.

Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayinsu a kai, dangane da ƙarin wa’adin mulkin na watanni shida kamar yadda babban lauyan ya bayyana.

Siyasa a Najeriya na ci gaba da zafafa yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2023.