Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaɓen 2023 da su ajiye aikinsu kafin ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al’adu ne ya sanar da hakan bayan taron FEC da Shugaba Buhari ya jagoranta a yau Laraba.
Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari’a), Godswill Akpabio (Neja Delta).

Haka zalika hadimin na shugaban ƙasa Tolu Ogunlesi ya tabbatar da umurnin na shugaban ƙasa ga ministoci masu son yin takara kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya wallafa cewa “yanzun nan dukkan ministocin fadar Shugaba Buhari da ke son yin takara za su yi murabus kafin ko ranar 16 ga watan Mayun 2022.”