Rundunar sojin Najeriya a Jihar Imo sun tabbatar da hallaka mutane hudu wanda ta ce ta na kyautata zaton “yan kungiyar IPOB ne masu rajin kafa kasar Biafara a karamar hukumar Orlu ta Jihar.

Daraktan Hulda da jama’a na rundunar sojin Burgediya Janar Onyema Nwachukwu shine wanda ya bayyana hakan ga manema Labarai.

Onyema ya ce a lokacin da lamarin ya faru sun samu nasarar kwato bindiga guda daya da kuma harsasai guda goma wayoyin hannu Mota da kuma Layu.

Burgediya Janar ya ce sun kai harin ne sakamakon “yan kungiyar ta IPOB da su ke matsanta wa mazauna yankunan zaman gida,tare da yin barazana ga rayuka da dukiyoyin su.

Onyema ya ce “yan kungiyar su ne wadanda su ka fara harbe-harbe a lokacin da su ka ga jami’an tsaro su na gudanar da sintiri a Jihar domin tabbatar da zaman lafiya.

Janar Onyema ya kara da cewa a yayin musayar wutar sun hallaka mutane hudu yayin da sauran su ka arce.

Onyema ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da su sanar da su duk wasu bayanai a lokacin da su ka ga wadanda ba su yadda da su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: