Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana aniyar ta zata ɗauki sabbin ma’aikata 3500 a faɗin jihar.

Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Kano a jiya Talata.
Ibn Sina yace wannan na zuwa ne bayan sahalewar da hukumar ta samu daga Gwamnatin jihar Kano, a wani mataki na ƙara inganta ayyukan hukumar ta Hisbah.

Babban kwamandan yace tsarin ɗaukar sabbin ma’aikatan zai baiwa ƴan Hisbah na sa kai da ake kira ‘Hisbah Marshal’ fifiko, kana daga bisani sauran mutane su shigo ciki.

A cewar sa:
“Kaso saba’in cikin ɗari za su kasance cikin Hisbah Marshal wanda shakka babu mun gamsu da irin ƙoƙari da gudunmawa da suke baiwa hukumar Hisbah daga ɗaukar su zuwa yanzu.
“Sai kuma shalkwatar hukumar ta Hisbah cikin tsarin jadawalin za ta ɗauki mutane ɗari biyar, sai ƙananan hukumomi na kwaryar birnin Kano guda takwas za su ɗauki ɗari-ɗari, sai kuma sauran ƙananan hukumomi da za su ɗauki hamsin-hamsin kowannen su.
Babban kwamandan hukumar ya kuma ja hankalin al’umma da su kaucewa faɗawa komar bata gari wajen karɓar kuɗin sun don sa su cikin tsarin ma’aikatan da hukumar za ta ɗauka nan ba da daɗewa.
“Duk mai son samun wannan dama to ya garzaya karamar hukumar sa, daga nan ne za’a ɗauka don turo mana sunayen mutane mu tantance.