A Karon farko Dalar Amurka ta yi tashin gwauron zabi a kan Naira inda a yau Lahadi dalar ta kai kimanin Naira ɗari shida da goma a kuɗin Najeriya a kasuwar bayan fage.

Rahotanni sun bayyana cewa, Duk da cewa farashin naira a hukumance kowacce ɗaya tana dai-dai da Naira ɗari huɗu da sha tara da kwabo biyu, sai dai a yau ana musayarta a kan wannan adadi.

Haka wani kamfanin canji kuɗi mai suna Aboki Forex, wanda ke da shafin yanar gizo da ƴan Najeriya ke sanin farashin canjin kuɗin ƙasashen ƙetare daga shi a kan farashin bayan fage, ya ruwaito cewa ana sayar da Dala kan Naira 610 a safiyar yau Lahadi.

Tun a ƴan watannin baya ne dai Naira ke ci gaba da faɗuwa matuƙar idan aka kwatanta ta da Dala.

A baya-bayan nan an samu tashin dalar daga Naira 588 kan kowacce Dala guda a ranar 8 ga wannan wata da muke ciki na Mayu, inda kuma a yau ɗin aka buɗe hada-hadarta a kan Naira 610 a cewar Aboki Forex.

Leave a Reply

%d bloggers like this: