Ƴan ta’addar Boko Haram sun yi wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC kwanton bauna, inda suka kashe ƴan sanda uku tare da raunata wasu huɗu.

Wata majiyar tsaron sirri sun shaida cewa maharan sun far wa ayarin motocin da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Maiduguri.
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun buɗe wuta kan ayarin motocin da ke ɗauke da ƴan sanda, haɗe da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress wanda har yanzu ba a tantance shi ba.

Ƴan ta’addan sun kuma ƙona motocin sintiri guda biyu da suke ciki, inda biyu daga cikin ƴan sandan suka mutu nan take yayin da ɗaya ya rasu a asibiti. Yanzu haka wasu huɗu suna kwance a asibiti.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kauyen Goni Matari da ke karamar hukumar Kaga a jihar Borno a ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu; Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Tein T.S. Jack-Rich, dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC sun je Borno a karshen mako.
Amma ba zan iya tabbatar da ko wane daga cikin masu neman takarar ba a halin yanzu ba. A cewar majiyar