An dawo da zirga-zirgar jiragen sama na babban filin tashin jiragen sama na Kaduna international airport bayan watanni biyu da rufewa.

Shugaban hukamar zirga-zirgan jiragen sama ne ya bayyana haka inda ya ce za’a fara jigilar fasinjojin jiragen kamar su Azman air da sauran su.
Ya ce ina maisanar da Al’umma an dawo da jigilar fasinjoji daga jiya Litinin tun bayan watanni biyu da aka rufe ba tare aiki ba.

A ranar 26 ga watan maris ne wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka farmaki filin jirigin tare da hallaka masu gadi yayin aikin su na tsaro wanda hakan ya kai ga dakatar da tashin jiragen domin inganta tsaro.

Amma dai-dai wannan lokaci duba da yadda lumuran tsaro su ka yi kyau shiyasa muka bada umarni a dawo da aiki ba tare da ɓata lokaci ba, za’a farawa daga jiya Litinin 23 ga watan Mayu
Masu garkuwan da mutanen da su ka yi garkuwa da kusan mutane 70 a jirigin ƙasan Kaduna zuwa Abuja sun bayyana sharaɗi kafin su saki waɗanda su ka sace
Masu garkuwan.
Ƴan bindigan sun tattaunawa da fittacen malamin addini Ahmad Abubakar Gumi ta wayar tarho sun bayyana cewa kwanaki 7 su ka baiwa gwamnati a biya musu buƙatar su ko kuma su hallaka mutane da su ka yi garkuwa da su.
Cikin saƙon muryar da su ka tattauna da malamin an jiyo wani daga cikin ƴan bindiga yana cewa dole gwmanti ta sakar musu ƴaƴansu guda 8 da aka kama a Kaduna.
A cikin sunayen ƴaƴan na su ya lissafa Biyar Abdurrahman, Bilkisu, Usman, Ibrahim da juwairiya.
Ya cigaba da cewa mutanen da su ka yi garkuwa da su suna cikin ƙoshin lafiya kamar yadda muka tura muku hotunan ta watsap amma ba biya mana buƙatar mu ba zamu ɗakko su ɗaya bayan ɗaya muna kashe su.
An yi garkuwa da fasinjoji ne a ranar 28 ga watan maris ɗin wannan shekarar da muke ciki a yayin ƴan bindigar su ka kaiwa jirgin ƙasan hari.
Sai dai a kwanakin nan Gwamnati ta sa ranar 24 ga watan mayu domin dawo da jigilar jirgin amma ta ɗage.
Wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar asiri ne ta Aiye sun kashe wani mutum mai suna wale matasaka a daren Litinin Jihar Ogun.
Jarida Vanguard ta rawaito cewa yankan rago aka yi masa akan babbar hanyar Qiuerra a cikin Abekuta.
Wannan na zuwa bayan kusan wata guda da hallaka wani mai suna Tommy wanda shima ɗaya daga cikin ƙungiyar asiri ne a Abekuta
Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa shima wale matasaka na daga cikin ƙungiyar ta asiri kuma ana zargin sun hallaka shine domin shi ne ya kashe Tommy.
Idan za a iya tunawa akalla mutane 15 aka hallaka waɗanda su ke da alaƙa da ƙungiyar ta asiri tun bayan hallaka Tommy amma ƴan sanda sun kama wasu daga cikin ƴan ƙungiyar ta asiri.
Rundunar ƴan sandan jihar Ondo ta tabbatar da kuɓutar uba da ɗansa da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar ɗin data gabata a jiya Litinin.
SP Fanmi Odunlami mai magana da yawun rundunar ta ƴan sanda shine ya bayyana haka a yau Talata ya ce Olu da ɗansa sun shaki iskar yanci.
Ya cigaba da cewa an saki uba da ɗansa ne jiya Litinin da misalin ƙarfe 12 30 na rana a cikin gari
Sannan ya ƙara da cewa ina mai sanar da ku cewa waɗanda aka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci sai dai ban sani ba ko iyalan waɗanda aka sakin sun biya kuɗin fansa ko akasin haka.
An yi garkuwa da uban da danna sa ne a yayin da su ke tafiya a babbar hanyar zirga-zriga ta garin na Jihar Ondo daga wasu da ake zargin ƴan garkuwa da mutane ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Sai dai tun da farko ƴan bindigan sun nemi a biya su Naira Miliyan Goma a matsayin kuɗin fansa amma iyalan sun ce za su biya Miliyan Ɗaya su kuma suka ki yarda da hakan.