Majalisar masarautar Gaya ta tuɓe Dagaci ƙauyen Gudduba da ke yankin ƙaramar hukumar Ajingi Mallam Usman Muhd Lawan.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na masarautar Malam Aminu Ahmad Rano ya fitar da tsakar ranar yau Laraba.
Sanarwar ta ce, Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda ya sanar da hakan ya ce bayan dogon bincike an samu Dagacin da hannu dumu-dumu wajen badaƙalar filaye.

Haka kuma sanarwar ta kuma umarci Madakin Gaya Alhaji Wada Aliyu da ya tura wakilin da zai kula da harkokin shugabancin kauyen.

Masarautar ta ƙara da cewa ba za ta saurara kan duk wani rashin adalci ko aikata wani abu da zai taɓa mutunci al’umma ko kuma masarautar ba daga masu riƙe da sarautun gargajiya.