Jam’iyyar APC mai mulki a Najwriya ta sanar da cewar mutane goma daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa sun faɗi yayin da aka fara tantance su.

Jam’iyyar APC ta fara tantance ƴan takara masu zawarcin kujerar shugaban kasa a yayin zaɓen shejarar 2023.
An fara aikin tantance yan takarar ne a ranar Litinin zuwa jiya Alhamis sai dai kwamitin bai bayyana sunayen mutanen da su ka fadi a yayin tantancewar ba.

Akwai yan takara da dama daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.

A na sa ranan jam’iyyar za ta gudanar da zaɓen fidda gwani a ranar 8 da 9 ga watan da mu ke ciki.