Rikici ya ɓarke a kasuwar Lungbe Timber da ke babban birnin tarayyar Najeriya bayan da wani ya yiu ɓatanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W.

Mutane sun yi gaggawar jefe shi tare da kone gawar mutumin da har yanzu ba a kai ga tantance shi ba.

Jami’an tsaro sun isa wajen da lamarin ya faru tare da harbin iska domin tarwatsa mutanen da ke wajen.

Idan ba a manta ba a jihar Sokoto ma an ƙone gawar wata ɗaliba da ta yi ɓatanci ga annabi Muhammad S.A.W.

Sai dai hukumomi a Najeriya sun bayyana hakan a matsayin ɗaukar doja a hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: