Hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta bayyana ranar karshe ga jam’iyyun siyasa na mika mata yan takaran shugaban kasa da mataimakansu.

Hukumar tace nan da ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni misalin karfe 6 na yamma, za’a rufe karbar sunan.
Amma na gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, an basu nan da ranar 15 ga watan Yuli, 2022.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a ganawarsa da kwamishanonin INEC na jihohi REC a yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Ya ce “Yau Alhamis, 9 ga watan Yuni, 2022 ne ranar karshen gudanar da zaben fidda gwanin dukkan jam’iyyun siyasa.”
Farfesa Yakubu ya kara da cewa su kuma Gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya, nan da ranar 15 ga Yuli, 2022.