Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa nan da shekarar 2030 mai zuwa za a daina ammafani da Ice da Kalanzir a Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya juma’a a lokacin da ya ke tattaunawa da shugaban kasar Amurka Joe Biden ta bidiyo.

Shugaban ya ce a shekarar ta 2030 din bayan daina amfani da Ice da Kananzir din gwamnatin a wannan lokacin za ta maye gurbin su da gas domin dakile yaduwar gurbatacciyar iska a Najeriya.

Buhari ya kara da cewa daga lokacin da Najeriya ta daina amfani da Itace da kananzir kasar za ta samu raguwar sauyin yanayi da kuma gurbatacciyar Iska da kashi 22 cikin 100 a shekarar ta 2030 mai zuwa.

Muhammad Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta na sane da irin illar da amfani da sinadari mai fitar da hayaki ke haifar  babbar illa a Najeriya,wanda kuma hakan ya sanya wasu kasashen duniya ke yunkurin daina amfani da sinadaran.

Shugaban ya ce a lokacin za a haramta kona bola a gonaki domin hana yaduwar gurbatacciyar iska sannan kuma za a dawo da sufurin motocin Bas na haya a hanyoyin Najeriya.

Shugaba Muhammad Buhari ya kuma shaidawa shugaban Amurca cewa Najeriya ta yi wasu sababbin gyare-gyare a dokar da ta gabatar a wani taron duniya wanda za a kawo karshen sauyin yanayi duba ga zamani.

Idan ba a manta ba a shekarar 2012 gwamnatin da masu hannu da shuni a bangaren da ya shafi man fetur a wancen lokacin ta fara yunkurin haramta amfani da Ice da kuma Kalanzir domin yin amfani da gas wajen yin girki da sauran amfani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: