Yan sanda a Jihar Jigawa sun bayyana cewa an sace mahaifiyar dan takarar majalissar dattawa mai wakiltar Jigawa ta tsakiya Tajjani Ibrahim Gaya.

Kakakin hukumar yan sandan Lawal shiisu ne ya bayyana ga manema labarai.
Hajiya jaja da ke zaune a karamar hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa ta shiga hannun masu garkuwa da mutane a safiyar Talata kamar yadda jaridar Leadership ta rawaito.

Lawal Shiisu ya ce maharan sun farmaki gidan mahaifiyar dan takarar ne a wasu awanni na wannan rana tare da tilastawa dattijuwar mai shekaru 70 tafiya da ita.

Wasu majiyoyi sun ce yan bindigan sun kai su 15 zuwa 20 su ka farma garin ɗauke da muggan makamai sannan su ka yi awon gaba da ita.
Kwamishinan yan sandan jihar Jigawa ya bayar da umarni cikin gaggawa domin kubutar da ita daga hannun ƴan bindigan.